<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>150</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1) Ya mutanen ƙasan nan, Musulmi da ama duk,
 Sai ku kasa kunnenku ga labarin cetonku.

[V2]
 KORUS
 Yesu shi ne Mai Ceto wanda Allah ya aiko
 Domin fansar ƴan Adam daga bautar zunubi.

[V3]
 2) Babu wani masoyi ko kuwa mai jin tausayi.
 Sai dai Yesu haifaffe, shi kaɗai Ɗan Allah ne.
 Korus

[V4]
 3) Jinin ransa ne ya bayar domin ceton duniya.
 Shi ya ɗauke zunubai, shi ya buɗe ƙofar rai.
 Korus

[V5]
 4) Sheƙa gunsa kuwa yanzu, ga shi yana jiranku.
 Tuba daga laifinku, nemi ceto wurinsa.
 Korus</lyrics>
<title>Ya Mutanen Ƙasan Nan, Musulmi da Ama Duk LW150</title>
</song>